An Haifi Hon. Gambo Gujungu a garin Gujungu na Karamar Hukumar Taura da ke tsakiyar jihar Jigawa a shekara 1972.
Hon. Gambo Gujungu ya fara katun firamare a mahaifarsa ta Gujungu a Gujungu Central Primary School. Kafin ya kammala yanayi irin na aikin gwamnati ya sanya shi tafiya garin Kaduna tare da mahaifinsa da sauran y’an uwansa domin ci gaba da aikin gwamnati yayin da shi kuma Hon. Gambo Gujungu ya samu shiga Sabon Gari Primary School a Kaduna.
Hon Gambo Gujungu ya shiga Makarantar Rimi Collage inda kuma a nan ya kammala karatunsa na gaba da Primary.
Daga nan Hon. Gambo Gujungu ya shiga Babbar Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna ( Kaduna Polytechnic KADPOLY ) inda ya samu shedar diploma ta kasa akan abin da ya shafi Hadin Kan Kasa (National Diloma in Cooperative). Hakazalika Hon. Gambo Gujungu ya yi Advanced Diploma in Marketing kafin daga bisani ya soma Babbar Diploma ta Kasa akan Harkar Kasuwanci (HND in Business Administration) duk dai a KADPOLY. Hon Gambo Gujungu ya sake yin National Diploma akan Ilmin Na’ura Mai Kwakwalwa (ND in Computer Studies) domin samun karin wayewa akan rayuwar yau da kullum.
Hon. Gambo ya samu karamar shedar karatu a kan ilimin kasuwanci na musamman (Social Business) International United Business School da ke Washington DC a Amurka.
Hon. Gambo Gujungu ya yi Postgraduate Diploma in Entrepreneurship. Sannan kuma ya yi Masters a kan Conflict Management. Duk a Jami’ar Jihar Kaduna (Kaduna State University).
Bayan nan Hon. Gambo Gujungu ya samu damar halartar bitoci na musamman da manyan taruka na musamman (Workshop, Seminars and Symposium and Retreat) a ciki da wajen Nigeria. Daga ciki hadda samun damar halartar taron wayar da kan mutane masu yawon bude ido na Duniya baki daya wato International Visitors Leadership Program (IVLP) wanda ya gudana a kasar Amurka a Shekara ta 2013.
Hon. Gambo Gujungu ya sake samun wani digirin a fannin Social Business a USA international Institute of Professional Exchange a kasar Amurka.
Hon. Gambo Gujungu ne shugaban hadaddiyar kungiyar matasan Arewa mai zamankanta wato (AREWA YOUTHS FORUM AYF) tun daga 2006 har yau din nan. A cikin wannan tsawon lokaci da Hon. Gambo Gujungu ya kwashe yana Shugabancin Kungiyar AREWA YOUTHS FORUM, ya samar da abubuwan ci gaba musamman da suka shafi tattalin Arziki da hadin kai da kawo tsaro da wayar da kan matasa a kan harkar siyasa da kasuwanci da samar da zaman lafiya a tsakanin matasa ta hanyar hada tarurrukan wayar da kan matasan a lokuta da gurare daban daban a Nigeria. Ya samarwa wannan kungiyar darajoji da daukaka masu yawa daga ciki hadda samun takardar yabo daga Embassy na Kasar Amurka dake Abuja. Daga shekarun 2014/2015 wannan kungiya ta Arewa Youths Forum ta samu damar gudanar da shiri mai suna CONFLICT MITIGATION AND PEACE BUILDING PROJECT (CMPB) a Jihohi hudu dake Arewacin Nigeria da suka hada da Kaduna, Nasarawa, Bauchi da Taraba. Wannan shirin ya taimaki Nigeria wajan kara hada kan matasa da kuma wayar da su Akan yadda ake yada hadin kai da zamantakeewar mutane babu tsangwamar juna wanda hakan ya sa matasa sama da Dubu Goma suka samu takardar zama jakadun zaman lafiya a yankunan su.
A yanzu haka Hon. Gambo Gujungu yana cikin mambobi na kwamatin tsaro na jihar Kaduna a matsayin jami’in sadarwa. Hakazalika a karkashin jagorancin Arewa Youths Forum, yana daga cikin mutanen da aka tattauna da su domin samar da COMMUNITY INTEGRATION AND CONFLICT TRANSFORMATION PROJECT (CICTP) a jihar Katsina.
Bayan kasancewar Hon. Gambo Gujungu shugaban Arewa Youths Forum tun daga 2006 har zuwa yanzu, hakazalika Gambo Gujungu shine Shugaban kungiyar AFRICAN YOUTHS CONGRESS. Kuma yana daga cikin Incorporated Trustee/Founding Member. Hakazalika member ne a kungiyar NIGERIAN YOUTHS ORGANIZATION. Hakazalika Hon Gambo Gujungu member ne a kungiyar Jigawa Forum a matsayin wakilin masarautar Ringim tun daga 2007 har yanzu. Bugu da kari Hon. Gambo Gujungu shine shugaban kungiyar AFRICAN YOUTHS SOCIETY daga 2012 har yanzu. Bayan haka Hon. Gambo Gujungu shine National Director Planning Police Community Relations Committee; Hakazalika Hon. Gambo Gujungu shi Board Member ne na National Agency For the Provision of Trafficking in Person (NAPTIP).
Hakazalika Hon Gambo Gujungu yana cikin Patrons na Golabal Foundation for Unity Peace and Development. Grand Patron na Golabal Education and Public Literacy Foundation. Grand Patron na Golabal Environment and Rural Integration Foundation. Kuma yana cikin Kungiyar da take kokarin kawo gyare-gyare da tsaretsare da sabunta Kungiyar Daliban Makarantar Kaduna Polytechnic KADPOLY.
A cikin Shekara ta 2019 kungiyar Independent Pan African Youths Parliament (IPAYP) a karkashin kungiyar Youth Civil for Society Organization in Africa ta nada Hon. Gambo Gujungu a matsayin mai magana da yawun bakin ta. Sannan ta bashi takarar yabon The African Achiever.
Hon. Gambo Gujungu babban dan gwagwarmaya ne musamman a akan abin da ya shafi matasa a ciki da wajen Nigeria.
SIYASA
Hon. Gambo Gujungu ya zama Board Member na NAPTIP a 2014 mukamin da tsohon shugaban kasa Jonathan ya nada shi.
Hon. Gambo Gujungu ya fada harkar siyasa gadan-gadan a shekara ta 2019 inda kuma ya zama mutum daya tilo da ya zama kamar wani ruwan dare mai gama duniya domin ya yi mamaya a mazabun Ringim da Taura a cikin kankanin lokaci inda ya zamana ko’ina ana labarin sa.
Shi Hon. Gambo Gujungu dogo ne kuma ba siriri bane, kuma ba baki bane ba fari bane. Yana da yawan fara’a da kuma yawan taimako. Yana da kwarjini da haba-haba da mutane.
Hon. Gambo Gujungu mutum ne da ba ya raina mutane, kuma baya yadda a raina shi.
Wadannan kyawawan halaye nasa sun taka rawar gani wajan jan hankalin mutane, inda suka nemi ya fito takarar dan majalissar tarayya mai wakiltar kananun hukumomin Ringim da Taura inda kuma ya amsa wannan kiran ya fito a zaben 2019.
Hon. Gambo Gujungu ya tsaya wannan takarar ne a Jam’iyyar PDP sai dai kash, kikijuna da muguntar da wasu daga cikin shuwagabannin jam’iyyar PDP reshen jihar da jagoran jam’iyyar suka yi, ya shafi wannan jajirtaccen matashin inda yana ji yana gani aka masa asarar nasararsa a 2019.
An yi ta gulmace-gulmace akan cewa Hon. Gambo Gujungu zai tafi yabar magoya bayansa sai kakar zabe ta dawo, amma ina, Hon Gambo Gujungu yana nan cikin jam’iyyar PDP, kuma tsagin Siyasa da Kulawa. Yana shiga cikin talakawa yana sa da zumunci da su, yana kuma taimakon su ta kowacce fuska.
Alhamdulillah Hon. Gambo Gujungu yana cikin gwarazan tafiyar siyasa da kulawa, wadanda ba sa gajiyawa wajen ba da gudunmawa da lokacinsu da hikimarsu da dukiyarsu da lafiyarsu, shi ya sa muke alfahari da shi muke kuma masa fatan Allah ya sa gobensa ta fi jiyansa kyau.
Daga: Haruna Shu’aibu Danzomo