For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamna Akeredolu Ya Faɗi Abun Da APC Zata Yi Ta Ci Shugaban Ƙasa A 2023

Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, SAN, ya gargadi jama’iyyar All Progressives Congress, APC, kan miƙa kujerar takarar Shugaban Ƙasa zuwa yankin Arewa.

A wani rubutu da yai a shafin Facebook a yau Alhamis, Akeredolu, wanda shine Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudancin Najeriya, ya buƙaci jam’iyyar ta tai iya bakin ƙoƙarinta wajen ci gaba da mulkin Najeriya ta hanyar miƙa kujerar takarar Shugaban Ƙasa zuwa yankin Kudu.

“Dole ne APC ta yi kokari ta ci gaba da mulki. Dole ne mu dinga juya bayar da dama domin mu ci gaba da samun dama!!! A miƙawa Kudu. . . . Shikena (That’s all),” in ji Akeredolu.

Baya da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da tsohon Gwamnan Jihar Lagos, Bola Tinubu, sauran masu neman APC ta tsayar da su takara sun haɗa da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da tsofin ministoci irin su Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Godswill Akpabio, da kuma Chukwuemeka Nwajiuba.

Gwamnoni masu ci da ke neman APCn ta amince musu tsayawa takarar sun haɗa da Kayode Fayemi (na Jihar Ekiti), Yahaya Bello (na Jihar Kogi), Dave Umahi (na Jihar Ebonyi), Ben Ayade (na Jihar Cross River) da kuma Badaru Abubakar (na Jihar Jigawa).

Sauran masu neman tsayawa takarar sun haɗa da tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Ken Nnamani, tsohon Kakakin Majalissar Wakilai, Dimeji Bankole, da kuma sanatoci masu ci da suka haɗa da Ibikunle Amosun, Ajayi Boroffice, da kuma Rochas Okorocha.

Wanda ya taya Shugaba Muhammadu Buhari a takara a shekarar 2011, Pastor Tunde Bakare, Uju Ken-Ohanenye, Nicholas Felix, Ahmad Rufai Sani, Tein Jack-Rich, Ikeobasi Mokelu su ma na neman samun damar tsayawa APCn takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

A watan Mayun da ya gabata ma, Akeredolu ya gargaɗi jam’iyyar APC kan miƙa kujerar takarar Shugaban Ƙasa zuwa yankin Arewa, inda ya ce, hakan zai jawo rigima.

A nasa ganin, yanzu juyin Kudancin Najeriya ne na fitar da Shugaban Ƙasa na gaba mai zuwa.

Akeredolu ya ce, yarjejeniyar da aka cimma lokacin da APC ta miƙa kujerun shugabancin jam’iyyar na ƙasa dole ne a bi ta.

Comments
Loading...