Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2023 na kimanin naira biliyan dari da saba’in da takwas da miliyan dari biyar (Biliyan 178.5) ga Majalissar Dokokin jihar a jiya Laraba.
Gwamnan ya ce an yiwa kasafin kirari da “Kasafin Kudin Hadinguiwa Domin Samun Cigaban Al’umma mai Dorewa na 2,”, wanda ake nufin hada kan kokarin gwamnatinsa domin kulawa da ci gaban da ake da shi.
Gwamnan ya kuma ce, an warewa manyan aiyuka a kasafin kaso hamsin cikin dari domin tabbatar da kudirin gwamnatinsa na samar da daidaito tsakanin kashe kudade da kuma sanya hannun jari.
Manyan aiyukan dai an ware musu naira biliyan 89.4 ne.
Ya kuma ce an warewa fannin ilimi naira biliyan 61.2 abun da ke a matsayin kaso 34.3 na kasafin, yayin da fannin lafiya kuma ya samu naira biliyan 28.9 kwatankwacin kaso 16.2 na jimillar kasafin.
A bangaren aikin gyaran tituna da gadojin da ambaliyar ruwa ta lalata kuma, gwamnan ya ce, an ware naira biliyan 19.65, yayin da aka ware naira biliyan 6.5 domin bunkasa aiyukan noma da kuma naira biliyan 4.95 domin samar da ruwan sha da tsaftar muhalli.
Gwamna Badarun ya ce cikin kudin da aka warewa fannin lafiya, za a yi amfani da naira biliyan 14.42 wajen karasa manyan aiyuka da kuma kaddamar da su a bangaren.
(NAN).