Daga: Saifuddin Madaci
Mukaddashin shugaban makarantar horas da malaman makaranta dake Gumel a jihar Jigawa, Dr. Dauda Abu Galadi, ya yabawa gwamnatin jihar bisa aiwatar musu da aiyukan cigaba a makarantar.
Da yake bayyana irin aiyukan da gwamnatin ta yi mu su yace, an shinfida musu hanyoyi a cikin makarantar masu tsawon kilomita 10, wanda ya bayyana hakan a matsayin abinda zai magance musu matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya.
Gwamnatin Muhammadu Badaru Abubakar ce ta yi musu wannan aikin, tare da gina wasu a jujuwa 4 na daukar darasi masu daukar dalibai 250, da dakunan kwanan dalibai maza da mata da gyaran ofishoshin wasu malamai, da kuma gina gadajen kananan malamai dana mayan malamai a makarantar da dai sauransu.
Haka kuma ya ce irin tunanin da mai girma gwamna ya dasa akwakwalen al’ummar jihar, na karasa aiki da wani ya fara a jihar, inda ya bayyana shi a matsayin mutum jajirtatce kuma mai zurfin tunani.
Kazalika Dr. Dauda ya bayyana bukatar dake akwai na basu damar daukar wasu malamai domin koyar da daliban ingantatcen ilimi mai nagarta.