For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamna Ganduje Ya Gabatar da Kasafin Kudin 2022 Na Sama Da Naira Biliyan 196

Gwamna jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2022 na sama da Naira Biliyan 196 ga Majalissar Dokokin Jihar Kano.

Abba Anwar, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Kano ne ya fitar da sanarawar hakan ga manema labarai a ranar Alhamis din nan.

Sanarawar ta ce, a jawabin da gwamnan ya gabatar gaban shugaban majalissar jihar, Hamisu Ibrahim Chidari, ya ce, Jimillar kudin aiyukan yau da kullum na shekarar 2022 shine Naira Biliyan 88,473,614,717.03 wanda ke wakiltar kaso 45% na kafatanin kasafin kudin.

Yayin da manyan aiyuka kuma za su lakume Naira Biliyan 107,879,853,788.07 domin manyan aiyuka a duk kanin sassan jihar.

Sashin ilimi yana da kaso sama da 26% na kasafin kudin wanda zai lakume Naira Biliyan 51.6.

Daga kasafin kudin na bangaren ilimi, za a warewa kudin abincin makarantun kwana Naira Biliyan 3.4 da kuma Naira Biliyan 2.2 domin manyan aiyuka a makarantun gaba da sikandire.

An kuma ware Naira Biliyan 33.8 domin gina titunan kasa da gadojin sama da gadoji da kuma tituna da dama.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, kasafin zai mayar da hankali kan tsare-tsaren gwamnati wanda zasu bunkasa tattalin arzikin jihar tare da kyautata rayuwar yayan jihar.

Haka kuma ya ce kasafin na 2021 yafi mayar da hankali kan ilimin yaya mata da fannin lafiya da manyan ayyuka da tsaro da kuma sauran bukatu nay au da kullum.

A fannin tara kudaden shiga ga jihar, gwamnan ya yi hasashen cewa adadin kudaden shigar da akayi has ashen tarawa sun kai Naira biliyan 146, da miliyan 844 da dubu 501 da 343.

Harajin kayayyaki ya kai naira biliyan 37 da miliyan 556 da dubu 575 da kuma wasu hanyoyin karbar kudade wanda suka kai Naira Biliyan 7 da miliyan 126 da dubu 367 fiye da shekarar 2021 da kaso 26.56 cikin 100.

Kasafin ya yi hasashen samun bashi na naira biliyan 22 da miliyan 368 da dubu 333 na naira 461 daga wajen jihar.

Daga cikin kudaden kasafin an ware Naira Biliyan 61 da miliyan 993 da dubu 825 da 929 domin biyan albashi da kudaden alawus-alawus ga ma’aikatan gwamnatin jiha dana kananan hukumomi da masu rike da mukaman siyasa da yan majalisun dokoki na jiha, da fannin shari’a da ofishin mai bincike na jihar da  

An kuma ware Naira miliyan 26 da dubu 479 da dari 788 da kobo 787 ga hukumomin gwamnati domin aiwatar da ayyukan cikin gida.

Comments
Loading...