For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamna Ganduje Ya Nada Sabon Sarkin Gaya

Gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwar nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a matsayin sabon sarkin masarautar Gaya.

Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya ba da sanarwar a gidan gwamnatin jihar.

Ya ce; “Bisa la’akari da karfin ikon da dokar masarautu ta 2020 ta Kano kamar yanda aka sabunta ta, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a matsayin sabon sarkin Gaya.”

Sakataren Gwanatin Kano ya kara da cewa; “nadin ya biyo bayan shawarwarin da masu nada sarki a masarautar Gaya suka bayar bayan gabatar da mutane 3 wanda daga cikinsu Mai Girma Gwamna ya nada Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a matsayin sarki.”

Kafin nadin sabon sarkin, shine Chiroman Gaya, wanda a yanzu ya gaji mahaifinsa Alhaji Ibrahim Abdulkadir wanda ya rasu yana da shekaru 91 a ranar Laraba 22 ga Satumba, 2021.

Comments
Loading...