Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya yi alƙawarin kawo sabbin tsare-tsaren noma a jihar don inganta harkokin noman da zai kai ga cimma tsarin samar da abinci na ƙasa a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a lokacin walimar karrama Kakakin Majalissar Jihar, Haruna Aliyu Dangyatin wadda aka gudanar a garin Miga na Ƙaramar Hukumar Miga.
Gwamnan ya ce, “Wannan gwamnatin zata tabbatar da kawo sauye-sauye na bunƙasa noma da sauran tsare-tsare da aka samar domin bunƙasa tattalin arziƙin jihar da walwalar jama’a.”
Gwamna Namadi ya ce, “Kamar yanda daminar bana ta fara, akwai buƙatar manoma su tuntuɓi malaman gona kan duk wata matsala da suka gani a gonakinsu, sannan kuma su yi amfani da dabarun noma na zamani da sauran dabaru domin su bunƙasa nomansu.”
Ya ƙara tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da samar da takin zamani, kayan feshi da sauran abubuwan zamani ga manoma a dukkan ƙananan hukumomin jihar guda 27.
Gwamnan ya kuma yabawa Ƙungiyar Ci Gaban Miga ta Miga Development Initiative Group da suka haɗa taron walimar domin karrama ɗansu Haruna Aliyu Dangyatin.
Gwamnan ya ƙara da cewa, “Ina taya mutanen mazaɓar Miga murnar cewa, Rt Hon Aliyu nagartaccen ɗan majalissa ne, jajirtaccen shugaba wanda yake son ci gaban Jihar Jigawa da ma ƴan’adam gaba ɗaya, saboda haka wannan karramawa ta dace.”
