For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamna Sani Bello Ya Isa Sakatariyar APC Domin Karbar Mulki Daga Hannun Mai Mala Buni

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello zai karbi shugabancin kwamitin rikon jam’iyyar APC daga hannun Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Gwamna Sani Bello yanzu haka ya isa Babbar Sakatariyar Jam’iyyar APC domin karbar shugabancin kwamitin riko na jam’iyyar.

Isarsa sakatariyar ya kawo karshen cece-kucen da ake kan karshen jagorancin Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.

A baya dai, Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC ta bakin Sakataren Kwamitin, Sanata James Akpan Udohedehe ya baiyana rade-radin cire Mai Mala Buni a matsayin labarin kanzon kurege.

Cire Mai Mala Buni dai na zuwa ne ‘yan makonni kadan kafin Babban Taron Zaben Shugabannin Jam’iyyar APC na kasa.

(NIGERIAN TRACKER)

Comments
Loading...