Jihar Jigawa mai shekaru 30 da watanni, wadda ta yi ‘sa’ar’ samo asali daga sananniyar jihar Kano ta kuma yi ‘sa’ar’ samun gwamnonin farar hula a mafi yawancin lokutan ta, sannan kuma ta kasance mai albarkatun kasar noma da yanayi mai kyau da kuma fadin kasa – tana da bukatu da za su iya banbanta da sauran jihohin Najeriya.
Jihar da take da kananan hukumomi 27 da garuruwa da kauyuka masu tarin yawa da kuma nisa tsakanin na farkonsu zuwa na karshensu duk ta inda mutum ya fara kirga. Jihar da take da masarautun gargajiya har guda 5 masu alaka da kuma banbanci a yanayi da ma wasu al’adun. Jihar Musulmai da ‘yan tsirarun Kiristoci da ma masu bin addinin gargajiya. Jihar Hausawa, Fulani da tsirarun Bare-bari da kuma wasu tsirarun bakin kabilun – tabbas akwai bukatar gwamna na musamman da ya fahimci jihar domin ya jagoranceta a 2023.
Jihar Jigawa ta yi fama da bangaranci na masarautu, har ma wasu na ganin a ita ne ake da kalmar ’emiratism’ kalmar da ko Bature bai tanade ta ba. Jihar ta yi fama da kalubalen talauci da karancin ilimi da ababen more rayuwa, wadanda suka samo asali daga shakulatun bangaro da garuruwanta suka fuskanta lokacin suna karkashin kulawar tsohuwar jihar Kano.
An samu karancin fitattu a jihar a bangaren malamta, boko, kasuwanci, aikin gwamnati da kuma sana’o’i. An samu karancin ababan more rayuwa a jihar kamar makarantu manya da kanana, asibitoci manya da kanana, tituna manya da kanana, tsarin samar da ruwansha a manya da kananan garuruwa. An samu karancin wadatuwar wutar lantarki a garuruwa.
Ofisoshin yin aiyukan da za su taso da ita ma an samu karancin su, hanyoyin samun kudaden shigar ta ma sun kasance cikin rudani. Guraren bincike kan makomar ta sun kasa komai, kwararrun da za su iya yi mata hange da tsara mata gwadaben samun cigaba sun guje mata – wasu suna Kano, wasu Kaduna, wasu Abuja, wasu ma gaba da nan, ba sa tunanin ta.
Tarihin jihar Jigawa cike yake da manyan kalubale musamman kafin dawowar mulkin demokradiyya a 1999. Shigowar demokradiyyar ta sa an samu canje-canje a wasu daga cikin matsalolin kuma masu kyau, wasu gudunmawar gwamnatin tarayya, wasu kuma kokarin gwamnonin da aka yi guda 3.
Cikin wadanda suka bar jihar, akwai wadanda suka guje ta akwai kuma wadanda sun barta ne dalilin nema ko aiki. Maganganun su ba sa zama hanyar tantance su, aiyukan su wajen cigaban jihar ko ‘yan uwansu da ke jihar shike fassara abin da suka yi. Zuwan 1999, da yawansu sun waiwayo jihar domin su samu dama a kan ‘yan jihar ko su samar da dama ga ‘yan jihar.
Shekaru 23 cikin demokradiyya, kaso kusan 80 cikin dari na wadanda suke jagoranta da wakiltar jihar irin wadancan wadanda suka bar jihar ne, sai dai duk kaso biyun sun yi kuma suna yi. Nasarorin da aka samu sun samo asali daga wadanda suka bar jihar domin aiki ko nema. Tsaikon da aka samu kuwa zai iya samo asali daga wadanda suka dawo jihar domin neman samun dama a kan ‘yan jihar.
Kafin rubutu na na gaba, ina ba mu shawarar fahimtar jihar mu, ‘yan siyasar mu, jam’iyyun mu da kuma sauran mu, domin mu kara gane ina zamu mika yardar mu a 2023. Sannan kuma mu dage da addu’ar Allah Yai mana zabin nagari mai kishin mu da kuma iya ciyar da jihar mu gaba.
A rubututtuka na na gaba zan dauki bukatun jihar mu a fannin ilimi, tattalin arziki, lafiya, da kuma tarbiyya domin bayyana abun da ake da shi, abun da ake bukata da kuma tunani na na irin gwamnan jihar Jigawa wanda zai iya – in Allah Ya yarda zan yi rubututtukan ta hanyar nuni ba tare da bayyana sunan dan takara ba ko jam’iyya ba, sai dai bayanan da za su iya nuni ga wani dan takara ko wata jam’iyya, shima hakan ba don talle ko adawa ba sai don bayyana gaskiya. Ku cigaba da kasancewa da ni.
Kabiru Zubairu
Birnin Kudu
Jihar Jigawa