For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnan Ebonyi, Umahi Ya Fadawa Buhari Kudirinsa Na Takarar Shugaban Kasa A 2023

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Umahi ya bayyana hakanne yau Talata ga ‘yan jaridun fadar Shugaban Kasa, bayan ganawarsa ta sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar da ke Abuja.

Ziyarar Umahi dai ta zo ne kimanin awanni 24 bayan Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu ya gana da Buhari inda ya bayyanawa shugaban kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 shi ma.

KU KARANTA: Zama Shugaban Kasa Shine Daddaden Burina – Tinubu Ga Buhari

Da ya fito daga ganawar tasa da Buhari, Umahi ya tabbatar da cewa ya tattauna batun takararsa da Buhari, wanda ya ce masa ya je ya nemi goyon bayan mutane.

Dave Umahi y ace, ziyarar Tinubu ta jiya ba ta sare masa guiwa ba, inda ya bayyana cewa takarar ba kawai tana ga manya ba ne.

Idan za a tuna, Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya bar jam’iyyar PDP ne a watan Nuwamba na shekarar 2020 inda ya koma APC.

Comments
Loading...