For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnan Jigawa Ya Jagoranci Tawaga Zuwa Taron Ƙoli Kan Tsarin Abinci Na Afirka A Kigali

Gwamnan Jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, ya jagoranci tawagar jihar zuwa taron shekara-shekara na Tsarin Abinci na Afirka na shekarar 2024, wanda aka fara a ranar Litinin a Kigali, Rwanda.

Halartar Gwamnan taron na nuna ƙudirin Jihar Jigawa na sauya fasalin noma, tabbatar da cin gashin kai wajen samar da abinci, da kuma haɓaka jihar ta zama abin koyi ga sauran jihohin Najeriya kamar yanda Mai Temakawa Gwamnan A Kafafen Sadarwa na Zamani Malam Garba Al-Hadejawy ya bayyana.

Taken taron na bana shi ne “Kirkira, Ƙaruwa, da Haɓakawa: Samar da Sauyin Tsarin Abinci a cikin Shirin Fasahar Zamani da Sauyin Yanayi.”

Wannan taron na gudana ne a tsakanin ranar 2 zuwa 6 ga watan Satumba, inda zai tattaro muhimman masu ruwa da tsaki don tattauna makomar tsarin abinci a Afirka.

Gwamna Namadi zai gabatar da jawabi na musamman a taron, inda zai bayyana dabarun Jihar Jigawa da kuma nasarorin da aka cimma wajen inganta samar da abinci da kuma dogaro da kai a fannin noma.

Haka kuma, tawagar Jihar Jigawa za ta halarci tattaunawa da masu ruwa da tsaki don nuna shirin “Rice Millionaires Project” na jihar, wanda ke taka rawa wajen tabbatar da tsaron abinci na ƙasa da kuma inganta samar da takin zamani.

Tawagar za ta kuma samu damar tattaunawa da jami’an gwamnati, abokan hulɗa, da masu zuba jari daga bangarorin kamfanoni masu zaman kansu, domin haɗa kai da kuma jawo hannun jari a fannin noma don bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Jigawa.

Comments
Loading...