For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnan Sokoto Tambuwal Ya Baiyana Aniyarsa Ta Takarar Shugaban Kasa A 2023

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya baiyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman zama Shugaban Najeriya a zaben shekarar 2023.

Tambuwal zai yi kokarin cimma burinsa ne ta hanayar jam’iyyar PDP.

Tshohon Kakakin Majalissar Wakilan ya baiyana hakan ne bayan wani zaman tattaunawa da yai da muhimman masu ruwa da tsaki yau a Sokoto.

Da yake jawabi kan tsayawa takarar, Tambuwal ya ce ba wai iya shirya yin takara ba, ya shirya tsaf domin magance tarun matsalolin da suke addabar Najeriya a matsayinsa na Shugaban Najeriya.

Ya baiyana cewa ya zama na daban, ba wai kawai a matsayinsa na gwamna ba, har ma a matsayinsa na Shugaban Majalissar Wakilai wanda ba a taba samunsa da zargin cin hanci da rashawa ba.

Tambuwal dai yanzu ya hau layin sauran ‘yan PDP da suka baiyana aniyarsu ta neman Shugaban Kasa wadanda suka hada da Danjarida, Dele Momodu, da Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad.

Idan za a iya tunawa, a zaben fidda gwani na PDP a takarar Shugaban Kasa na shekarar 2018, Tambuwal shine ya zo na biyu bayan Atiku Abubakar da yaiwa jam’iyyar takara a zaben 2019.

(Vanguard)

Comments
Loading...