For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnati Ta Janye Ƙarar Da Ta Kai Shugabannin Ƙwadago, Akwai Yiwuwar Fasa Yajin Aikin Da Za A Fara 14 Ga Wata

A jiya Litinin Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta kai Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, da Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, tana zarginsu da saɓa umarnin kotu, inda suka gudanar da zanga-zanga a ranar 2 ga watan Agusta, 2023, kan janye tallafin man fetur, bayan kotu ta hana hakan.

Janyewar dai na zuwa ne bayan Ma’aikatar Shari’a ta yi ƙarar shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon kan zargin cewar sun yi gaban kansu wajen saɓa umarnin kotu da ya hana su yin zanga-zanga amma su ka jagoranci zanga-zangar.

Kotun Ɗa’ar Ma’aikata ta Ƙasa dai, ta hana haɗakar ƙungiyoyin ƙwadagon shiga yajin aiki tun a baya, to amma lauyan nan mai kare haƙƙin bil’adama, Femi Falana ya ce, ƙungiyoyin zasu iya yin zanga-zangar da suka shirya.

A ranar Larabar da ƙungiyoyin suka jagoranci zanga-zangar ne suka sami ganawa da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, inda shugaban ya tabbatar musu da cewar zai biya musu buƙatunsu sannan zai rage raɗaɗin da ake ji dalilin janye tallafin man fetur.

To sai dai duk da haka, Ma’aikatar Shari’a ta Ƙasa ta garzaya kotu domin gurfanar da shugabannin ƙwadagon bisa zarginsu da saɓa wancan umarni na kotu, abin da ya fusata ƙungiyoyin inda har su kai barazanar shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Agustan nan da muke ciki.

To amma, a yanzu, Ma’aikatar Shari’ar a jiya Litinin ta ce, gwamnatin ta fasa tuhumar shugabannin ƙwadagon da laifin saɓa umarnin kotun, abin da ya sa ake tunanin ƙungiyoyin ƙwadagon na iya fasa shiga yajin aikin da suka ce zasu shiga a ranar Litinin mai zuwa.

Comments
Loading...