For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Buhari Ba Ta Da Sha’awar Bayyana Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta’addanci – Femi Adesina

Daga: Abu Hammad Hadejia

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da sha’awar bayyana suna da kuma kunyata duk wani da ke da hannu wajen daukar nauyin ‘yan ta’adda a kasar nan.

Mista Adesina, wanda ya bayyana hakan yayin gabatar da shirin talabijin na Channels a ranar Litinin, ya ce gwamnatinsu a yanzu ta fi sha’awar gurfanar da irin wadannan mutane a gaban shari’a.

Ya ce: “bayyana suna da kunyatarwa ba za su zama hujjoji ba, maimakon haka, gabatar da masu laifi a gaban shari’a zai kasance mafi dacewa.

“Za ku ga cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta fitar da wasu sunaye, kuma Babban Lauyan Tarayya (Abubakar Malami) ya yi bayani a kai yana mai cewa, duk wadannan mutane za a gurfanar da su a gaban koto nan ba da jimawa ba.

Comments
Loading...