Kudirin Kasafin Kudi na shekarar 2022 ya nuna cewa Fadar Shugaban Kasa za ta kasha Naira Biliyan 1.6 wajen siyan Ababan hawa da kuma kayan gyaransu.
Shugaban Muhammadu Buhari zai kuma kasha Naira Tiriliyan 2.3 wajen yawace-yawace a ciki da wajen Najeriya a shekarar ta 2022.
Wadannan adadi na kunshe cikin Kudirin Kasafin Kudin shekarar 2022 da Shugaba Buhari ya gabatarwa Majalissar Najeriya a Alhamis din da ta gabata
Kasafin da yawansa ya kai Naira Tiriliyan 16.39 yana da gibin Naira Tiriliyan 6.26.
Gwamnatin Buharin ta ce za ta ciyo bashi domin cike gibin kasafin, lamarin da yak e shan suka daga kalolin mutane da dama.
Haka kuma kasafin ya nuna za a kashewa jiragen Shugaban Kasa Naira Biliyan 12.5 a shekarar ta 2022.