Gwamnatin Jihar Jigawa ta nemi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, EFCC da kuma Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafen Al’umma da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC da su binciki matsayar wasu kadarorin da jihar ta gada lokacin da aka cire ta daga Jihar Kano a 1991.
A takardu mabanbanta da Kwamishinan Aiyuka na Musamman, Auwal Sankara ya sanyawa hannu, gwamnatin Jigawa tana neman hukumomin na yaƙi da cin hanci da su fayyace matsayar wasu filaye guda biyu da kadarorin gidajen gwamnati shida da ke Jihar Kano waɗanda suke mallakin Jihar Jigawa ne.
Da yake kokawa wajen jan ƙafa da ake samu wajen ganin Jihar Jigawa ta amfani kadarorin, Sankara ya bayyana cewa, duk ƙoƙarin da akai a baya ya ci tura.
Ya ce, “Kamar yanda kuka sani, an ƙirƙiri Jihar Jigawa ne daga tsohuwar Jihar Kano a 1991. Bayan ƙirƙirar Jihar Jigawa, akwai rabon kadarori da aka yi tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da ta Jihar Jigawa.
“Saboda haka, babu daɗi ka ga cewa rabon kadarorin na ta jan ƙafa, duk da ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi domin ganin an rabu lafiya a lamarin.
Ku Karanta Wannan: Kuton Ɗaukaka Ƙara Ta Kori Ƙarar Da Ake Wa Sule Lamido
“Saboda haka, ina sanar da ku cewa akwai kadarorin da har yanzu ba su zo garemu ba, kuma akwai buƙatar sanya bakinku a ciki.
“Kadarorin da ake magana a kai sun haɗa da fili mai lamba 133 a wani ɓangare na TP/UDB/173 a Farm Centre da kuma waɗannan Gidajen Gwamnatin da aka baiwa Jihar Jigawa masu lamba: GP 447 Suleiman Crescent, GP 897 Titin Maiduguri, GP 982 Titin Maiduguri, GP 891 Titin Maiduguri, GP 827 Titin Sokoto, da GP 874 Sharada,” in ji wasiƙar.
Auwal Sankara ya bayyana cewa an baiwa Jihar Jigawa waɗannan kadarori ne a lokacin rabon kadarorin da aka gudanar ranar 5 ga watan Mayu, 1993, a cikin yarjejjeniyar da Gwamnan Kano, Kabiru Gaya da Gwamnan Jigawa Ali Sa’ad Birnin Kudu suka sanyawa hannu.
Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi iya bakin ƙoƙari ta sasanta maganar ta hanyar tura wasiƙu zuwa Gwamnatin Kano amma har yanzu abin ya ci tura.
Wannan ce ta sa Jihar Jigawa neman EFCC ta shiga lamarin tare da sanya Gwamnatin Kano miƙa kadarorin ga Gwamnatin Jigawa, abin da ya ce idan ya faru za a samu ci gaban zaman zumunci tsakanin jihohin guda biyu.
