Gwamnatin Jihar Jigawa ta gargadi ƴan jihar kan shafin daukar ma’aikata ta yanar gizo wanda yake ta zagayawa a matsayin na bogi.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jiha, Ismaila Ibrahim ne ya sanar da haka a Dutse babban birnin jihar.
Sanarwar ta sa ta ce, wasu ƴan damfara na sanya tallalluka a wasu shafukan yanar gizo na bogi, suna bukatar ƴan Jigawa masu BSC, HND da ND su cike domin neman aiki a jihar.
Ya ƙara da cewa, haka kuma, ƴan damfarar na bukatar kuɗaɗe domin turawa mutane bayanansu.
Ya ce, gwamnatin Jihar Jigawa ba ta bayar da umarnin yin haka ga kowanne irin mutum ko kamfani ba.
Saboda haka, ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da maganar gaba ɗaya.