Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya kafa cibiyoyin kula da ciwon ƙoda guda biyar a jihar, kamar yanda Kwamishinan Lafiya, Dr. Muhammed Kainuwa ya bayyana.
Kainuwa ya bayyana hakan ne a Dutse yayin buɗe taron karɓar takardun neman kwangilar gina cibiyar gwaje-gwaje da kammala asibitocin ƙwararru na Hadejia da Kazaure.
Kwamishinan ya ce za a kafa cibiyoyin kula da ciwon ƙodar a hedikwatar masarautun Dutse, Hadejia, Kazaure, Ringim, da Gumel, inda ya ce gwamnatin ta ware Naira miliyan 500 domin waɗannan cibiyoyi.
Ya ƙara da cewa, za su aiwatar da wankin ƙoda kyauta ga dukkan marasa lafiya a jihar.