For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci, Yayin Da Fursunoni 1,576 Cikin 1,718 A Jihar Matasa Ne

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce, akwai matasa ƴan fursuna guda dubu 1,576 da ke zaman gidajen yari a jihar cikin fursunoni dubu 1,718 da ake da su a gidajen yarin jihar.

Kwamishinan Shari’a na Jihar, Barrista Dr. Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai a jiya Asabar.

Ya bayyana cewar gwamnati ta damu kan irin yawan matasan da ke zaman waƙafi a gidajen yarin jihar.

Dr. Musa ya ce abun damuwa ne a ce cikin fursunoni dubu 1,718 da ake da su a Jigawa, fursunoni dubu 1,576 duk matasa ne da ke shekarun tsakanin 18 zuwa 45.

Kwamishinan ya kuma ce, Gwamnatin Jihar Jigawa ta himmatu wajen ganin ta ƙara ingantsa Ma’aikatar Shari’a ta jihar domin samun ingantaccen aiki.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kano Za Ta Raba Littattafai Miliyan 3 A Makarantu, Za Ta Kuma Ginawa Malamai Gidaje

Ya ce, ‘ƙudire-ƙudire huɗu’ da ake da su a ɓangaren shari’a na Jihar Jigawa, sun haɗa da sake fasalin gidajen gyaran hali.

Ya ce za a duba wasu daga cikin dokokin jihar domin tabbatar da cewar sun dace da zamani sannan kuma za a ƙaddamar da amfani da dokar magance manyan laifuka haɗin guiwa da jami’an tsaro da sauran ma su ruwa da tsaki.

Ya kuma ce, za a kafa kwamiti domin duba yanda ake gudanar da hukunce-hukuncen manyan laifuka.

Ya kuma ce za a ƙirƙiri hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar, sannan kuma za a bai wa wayar da kan jama’a muhimmanci sosai.

Ya buƙaci gudunmawar ƙwararrun masana shari’a, alƙalan da su ka yi ritaya, malaman manyan makarantu, abokan hulɗa na ƙasashen waje, ƴan ƙungiyoyi, shugabannin addinai da na gargajiya da sauran al’umma wajen ganin an cimma nasarar abubuwan da aka sa a gaba.

Comments
Loading...