Gwamnatin Jihar Kano a jiya Laraba ta amince da bayar da hutun Babbar Sallah na tsawon kwanaki goma ga makarantun gwamnati da masu zama kansu a jihar.
Jawabin da mai magana da yawun Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Aliyu Yusuf ya fitar ya nuna cewa, hutun zai fara daga ranar Alhamis 7 ga watan Yuli ya kuma kare ranar Lahadi 17 ga watan na Yulin shekarar 2022.
Aliyu Yusuf ya kuma yi kira ga iyayen dalibai da kuma daliban da su yi biyayya ga tsarin hutun.
Ya kuma bayyana cewa, Ma’aikatar ta kuma umarci duk ƴan SS3 da ke rubuta NECO, NABTEB da NBAIS da kuma daliban musaya daga wasu jihohi da ke GSS Gwarzo da GGSS Shekara da su kasance a makarantunsu.
Ya ce, ma’aikatar ta umarci duk shugabannin makarantun firamare da sikandire da su tabbatar da cewa ƴan bodin sun dawo makaranta a ranar Lahadi 17 ga watan Yuli yayin da su kuma ƴan jeka ka dawo su dawo ranar Litinin 18 ga watan Yuli, 2022 saboda harkokin karatu zasu ci gaba yanda ya kamata daga ranar da aka dawo.
Aliyu Yusuf ya kuma ce, ma’aikatar ta yi gargadin cewa za a dau matakin da ya dace kan dukkan wadanda suka saba ka’idar da aka shinfida.