For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Kano Ta Maka  Ganduje, Ɗansa Da Matarsa A Kotu Kan Zargin Badaƙala Da Kuɗaɗe

Gwamnatin Jihar Kano ta maka tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat Umar da ɗansa Umar Abdullahi Umar da wasu mutane biyar a kotu kan zarge-zarge guda takwas da suke da alaƙa da cinhanci da rashawa, badaƙala da karkatar da kuɗaɗen da yawansu ya kai biliyoyin nairori.

Wannan na ƙunshe ne a takardar tuhuma mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Afrilu, 2024 da jerin shaidun mai shigar da ƙara a haɗe.

Jerin waɗanda ake zargin sun haɗa da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Enterprises Limited.

Ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen ya nuna cewar, a wani lokaci wajejen 10 ga Janairu na shekarar 2016 ko kusa da haka, a Kano, a Hukumar Shari’a ta Kano lokacin yana gwamnan jihar ya nemi cin hanci tare da karɓar kuɗi kimanin dala 200,000 a matsayin wani kuɗin morarsa daga wajen ɗaya daga cikin ƴan kwangilar da suke yi wa Jihar Kano Kwangila.

Takardar tuhumar ta ce, wannan abu da Ganduje yai ya zo daidai da aikata laifin cinhanci da rashawa wanda ake hukunta wa a Sashi na 22 na Dokar Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Al’umma da Magance Cinhanci da Rashawa ta Jihar Kano.

Comments
Loading...