Gwamnatin Jihar Kano ta soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke faɗin jihar.
Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne a ranar Asabar da ta gabata, a lokacin zaman tattaunawa tsakaninta da masu makarantu masu zaman kansu a jihar.
Mai Bayar da Shawara ga Gwamnan Kano kan Makarantu Masu Zaman Kansu da Na Sa Kai, Alhaji Baba Umar ne ya bayyana hukuncin, inda ya ce, ana buƙatar dukkan makarantu masu zaman kansu su cike sabon fom na rijista da gaggawa, saboda gwamnati ta samar da sabbin hanyoyin bayar da rijistar.
Baba Umar ya bayyana cewa, matakin ya zo ne domin buƙatar gwamnatin Kano na ta tabbatar da makarantu masu zaman kansu na bin dokoki da ƙa’idojin da suke aiki a jihar.
KARANTA WANNAN: Wadda Ta Fi Kowa Cin JAMB Ta Samu A Guda 8 Da B Guda 1 A WAEC
Ya ce, an tunawa masu makarantun kan tsarin biyan kaso 10 cikin 100 na kuɗaɗen da suke samu a matsayin haraji ga gwamnati, inda ya jaddada cewar, wannan na bayar da damar ƙara inganta harkar ilimi a jihar.
Baba Umar ya kuma yi alƙawarin kulawa da makarantun cikin gaskiya da adalci ba tare da nuna wariya ba, sannan kuma ya yi kira ga masu makarantu masu zaman kansu da su bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa a ɓangaren ginin makarantun, wajen ɗaukar darasi, manhaja da kuma lokutan karatu.
Ya kuma tabbatarwa da iyaye cewar, an matuƙar ba su muhimmanci wajen kare martabarsu da ta ƴaƴansu a al’amarin makarantun.
A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, Alhaji Muhammad Adamu, yabawa gwamnatin ya yi kan yunƙurin bunƙasa tafiyar makarantun, sannan kuma yai kira ga masu makarantun da su haɗa kai da gwamnati domin tabbatar tsarukan da aka kawo.