Majalissar Jihar Kano ta amince da kudirin samar da gidaje 5000 domin malaman makaranta, ma’aikatan gwamnati da kuma sauran ma’aikata a jihar.
Da yake karanta takardar kudirin, Kakakin Majalissar Jihar Kano, Hamisu Ibrahim Chidari ya ce, Majalissar Zartarwar Jihar Kano tana bukatar a amince mata domin ta samar da gidajen a dukkanin kananan hukumomin jihar guda 44.
Bayan yin dogon nazari, ‘yan majalissar sun amince da kudirin samar da gidajen karkashin kulawar Shugaban Hukumar Kula da Aiwatar da Tsare-tsare da Aiyuka, Rabi’u Sulaiman Bichi.