Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta hana duk wasu masu shekara kasa da 18 mallakar layin waya.
Wannan ya fito ne a kwafin takardar fitar da sabbin tsare-tsare na dokokin masu anfani da layikan waya, wanda hukumar ta fitar a shafinta na yanar gizo.
A sabbin dokokin, NCC ta ce iya ‘yan shekara 18 zuwa sama ne za su mallaki layin wayar.
“Mai amfani da layin waya, na nufin mutumin da bai gaza shekara 18 ba, kuma ya mallaki layin wayar ta hanyar siya ko ya shiga wata yarjejjeniya da kamfanin da aka amincewa.
Wadannan dokoki an sanyasu ne la’akari da karfin ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa hukumar NCC a sashi na 70 na Dokar Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta shekarar 2003.