Hukumar Kula da Kaidojin Hada-Hadar Kudade Fiscal Responsibility Commission (FRC) ta ce ta sanar da kusan bankuna 14 da guraren hada-hadar kudade wadanda ke bayar da bashi ba tare da bin ka’idar da ta dace ba.
Shugaban Hukumar, Victor Muruako ne ya sanar da hakan a taron da aka gabatar kan Wayar da Kai Wajen Gudanar da Gwamnati a Bude da Tsantseni domin ‘yan yankin Kudu maso Yamma a Lagos a ranar Litinin din nan.
Taron wayar da kan na kwana biyu yana da take “Gudanar da Gaskiya a Harkar Kudade da Samar da Cigaba mai Dorewa ga Yankunan Kasa.”
FRC ce ta shirya taron a matsayin daya daga cikin tarurrukan wayar da kai kan aiki da gaskiya, rikon amana da hangen nesa Transparency, Accountability and Prudence (TAP) a harkokin kula da kudaden al’umma.
A jawabin maraba, Muruako ya ce, hukumar FRC ta riga tana duba hukumomin bayar da bashi sannan kuma duk wadanda aka kama da lefi za a dakatar da su.
Duk da dai ya ki bayyana sunayen bankuna da guraren da abin ya shafa, shugaban ya bayyana cewa hukamar ta sa na cigaba da tattaunawa da kamfanonin.
A cewarsa, akwai ka’idoji da dole jihohi su cika su kafin a ba su bashi.
“Bankuna da sauran guraren hada-hadar kudaden da suka mayar da kansu hanyar rashin kulawa a harkokin kudade wajen bayar da bashi ga bangarorin mulkin kasa ba tare da bin ka’ida ba, za a dakatar da su.
“Bayar da bashi, karbar bashi da rashin biyan bashi suna cikin dokokin da suka shafi gwamnatin tarayya ne a kundin tsarin mulkin kasa na 1999 wanda akaiwa gyara.
“Sashi na 42(2) a kaso na X na dokar kula da ka’idojin hada-hadar kudade ta 2007, ya fayyace tsare-tsare na karbar bashi ga gwamnatoci a kasa ko hukumominsu da kuma kamfanoni.
“Bayar da bashi da bankuna da guraren hada-hadar kudade ke yi da ya saba da wannan sashi to abu ne da ya saba ka’ida,” in ji shi.
Ya ce gwamnatocin kananan bangarori bai kamata su mayar da karbar bashi a matsayin dama ta karshe ta cike gibin kudade ba, kamata yai su nemi hanayar samun kudadensu a cikin gida.
“Duba da abubuwan da suka gabata, hukumarmu na sanar da bankunan da suka sab ka’ida da sauran guraren hada-hadar kudade cewa damar yin abin da bai dace ba a kulle ta ke.
“Za mu tabbatar da hukuncin doka kan duk abin akai wanda ya saba ka’ida ko ina kuwa akai hakan.
“Idan kuma muka samu guraren da dokar Kula da Hada-hadar Kudade ta 2007 ta gaza kawo gyara, to za mu yi amfani da hadin kan da muke da shi da hukumomin ICPC da EFCC.”
Da yake jawabi, Shugaban Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa EFCC, Abdurrashid Bawa, ya ce ya kamata jihohi su tabbatar da dokar Kula da Hada-hadar Kudade a cikinsu.
Bawa, wanda ya sama wakilcin Mataimakin Kwamanda na EFCC na jihar Lagos, Emeka Okonjo, ya ce ya kamata jihohi su dauki harkokin gaskiya da yin aiki bisa doka da matukar muhimmanci.
A nasa jawabin, Shugaban Hadakar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Mummunar Gwamnati, Coalition Against Corruption and Bad Governance (CACOBAG), Toyin Raheem, ya koka da yanda wasu jihohin suka ki aiwatar da dokar kula da hada-hadar kudade a cikinsu.
Raheem, wanmda yai magana a madadin kungiyoyi masu zaman kansu, ya ce kulawa wajen magance matsalar cin hanci da rashawa aiki ne na duk ‘yan Nigeria.
“Domin a gina kakkarfar Nigeria, dole ne duk mu kasance cikin al’amuran gwamnati mu kuma bukaci karin bayani daga shugabannin mu a kan kudade da yanda suke kashe su.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Nigeria NAN ya rawaito cewa, wakilan Hukumomin Kudade na Nigeria a yankin Kudu masu Yamma, da kuma wakilan Kwamitocin Samar da Daidaito da Bin Ka’ida na majalissun jihohin Kudu maso Yamma.
NAN