For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ba Ta Cika Alkawarin ASUU Ba Yayin Da Wa’adin Da ASUU Ya Bayar Ya Kare

Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen kare tunduma yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU tai alkawarin shiga bayan karewar wa’adin sati ukun da ta bayar ya kare.

A ranar Lahadin jiya ne wa’adin da ASUU ta bayar ya kare, inda tai alkwarin cewa idan har ba a samu dai-daito tsakaninta da gwamnatin tarayya ba to za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Idan za a iya tunawa, a ranar 15 ga watan Nuwamba ne kungiyar ASUU ta baiwa gwamnatin tarayyar wa’adin sati uku domin cika alkawuran da akaiwa kungiyar.

Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya sanar da jaridar PUNCH a ranar Lahadi cewa, ma’aikatar ilimin ta rubutawa ma’aikatar kudi takarda kan batun biyan kudaden alawuns ga malaman jami’o’in.

Sai dai kuma bangaren kungiyar ASUU ya sanarwa jaridar PUNCH cewa alkawari daya kacal gwamnatin tarayyar ta iya cikawa kungiyar kawo wannan lokaci.

Gwamnatin tarayyar dai a baya ta yi alkawarin biyan Naira Biliyan 30 domin aiyuka a jami’o’i da kuma Naira Biliyan 22.1 a matsayin alawuns na ma’aikata.

Lokacin da aka tambayi shugaban ASUU, Farfesa Victor Emmanuel Osodeke kan matsayarsu bayan karewar wa’adin ya bayyana cewa za su tuntubi sassansu na jihohi kafin yanke hukunci.

Comments
Loading...