For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ba Ta Mutunta Yarjejjeniyar Mu – ASUU

Reshen Kungiyar ASUU na yankin Kano, wanda ya hada da jami’o’in gwamnati da ke jihar Kano, Kaduna da Jigawa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta mutumta duk yarjejjeniyar da akai da ita.

A takardar bayan taron da Ko’odineta na Kungiyar reshen Kano, Abdulkadir Muhammad ya sanyawa hannu, an bayyana cewa, a ranar Laraba reshen kungiyar ya bibiyi yarjejjeniyar da uwar kungiyar ASUU ta kasa tai da gwamnatin tarayya a watan Disamban 2020 domin ganin irin cigaban da aka samu.

Yarjejjeniyar Disamban ta shafi batutuwan da suka hada da samar da kudaden farfado da jami’o’in gwamnati, alawuns na malamai, al’amuran jami’o’in jihohi, cika alkawarin yarjejjeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta 2009, manhajar biyan malaman jami’o’i ta UTAS, rike albashin wasu malaman, tsarin ziyarar koyarwa da sauran batutuwa.

A bangaren kudaden farfado da jami’o’i, gwamnatin ta yi alkawarin bayar da Naira Biliyan 30 daga cikin Naira Biliyan 220 da akai alkawari a 2013 kafin karewar watan Janairu na shekarar da muke ciki.

To sai dai ga mamakin kungiyar, Naira Biliyan 20 kacal gwamnati ta iya fitarwa kawo wannan lokaci, wanda hakan ke nuni da rashin mutumta alkawarin da tai, ballantana kuma na gaba.

A bangaren alawuns na koyarwa da malaman ke bi kuwa, gwamnatin tarayyar ta yi alkawarin  bayar da Naira Biliyan 25 a watan Mayu na 2021, amma kawo wannan lokaci, gwamnatin ba ta saki kudaden ba.

Reshen ASUU na Kano ya bayyana cewa, gwamnatin a kwanakwanan nan ta saki Naira Biliyan 22.127 a matsayin alawuns na koyarwa ga malaman kamar yanda yake kunshe a kwarya-kwaryar kasafin kudi na 2021.

Reshen kungiyar ya nuna cewa babu wata yarjejjeniya da kungiyar ASUU tai da gwamnatin tarayya wadda gwamnatin tarayya ta mutumta 100 bisa 100.

A karshe, reshen kungiyar ya ce kungiyar ASUU a shirye take wajen ganin cewa ta ceci harkar ilimin jami’o’i a Najeriya.

Comments
Loading...