Kwamitin Rarraba Kuɗaɗen Tarayya, FAAC, ya ce ya raba naira tiriliyan 1.2 da aka samu a matsayin kuɗin shiga a watan Agustan 2024 ga Gwamnatin Tarayya, jihohi, da ƙananan hukumomi a Najeriya.
An raba kuɗin ne a lokacin taron FAAC na watan Satumba 2024 da aka gudanar a Abuja, kamar yanda sanarwar da Darektan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Bawa Mokwa, ya fitar ta bayyana a jiya Talata.
Adadin kuɗin da aka raba ya nuna raguwa da kashi 11 cikin 100 ko kuma naira biliyan 155 daga naira tiriliyan 1.358 da aka raba a watan Yulin da ya gabata.
Sanarwar ta ce, “Jimillar naira tiriliyan 1.203 da aka samu a watan Agustan 2024 an raba ta ne ga Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.”
Bawa Mokwa ya ce kuɗin ya haɗa da kuɗin shiga na naira biliyan 186.636, naira biliyan 533.895 daga harajin VAT, naira biliyan 15.02 daga harajin mu’amalar kuɗi ta intanet, da kuma naira biliyan 468.25 daga banbancin da aka samu na canjin kuɗaɗe.
Bawa ya ƙara da cewa daga cikin jimillar naira tiriliyan 1.203 da aka raba, Gwamnatin Tarayya ta samu naira biliyan 374.93, jihohi kuma sun samu naira biliyan 422.86, yayin da ƙananan hukumomi suka samu naira biliyan 306.53.