For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Raba Kudin Maris Naira Biliyan 714.629

Kwamitin Rarraba Kudaden Tarayya, FAAC, ya raba naira biliyan 714.629 ga rukunonin gwamnati uku na Najeriya jiya Laraba a Abuja a matsayin kudin watan Maris.

Wannan labari ya samu ne daga sanarwar bayan taro da aka saki a karshen zaman FAAC na watan Afrilu.

Mai magana da yawun kwamitin, Stephen Kilebi ya bayyana cewa, kudaden da aka rarraba sun hada da kudaden da aka samu ta hanyar haraji wanda ya kai naira biliyan 497.448; kudaden harajin VAT wanda ya kai naira biliyan 202.693; da kuma cajin hadahadar kudade ta banki, EMTL, wanda ya kai naira biliyan 14.488.

Cikin kudaden da aka raba, Gwamnatin Tarayya ta samu naira biliyan 276.141; jihohi 36 na Najeriya sun samu naira biliyan 232.129, yayinda kananan hukumomi 774 suka samu naira biliyan 171.257.

Jihohin da suke samar da mai sun samu karin naira biliyan 35.102 a matsayin kaso 13 cikin 100 na ribar mai.

NAN

Comments
Loading...