For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Na Kashe Naira Biliyan 18.397 Kullum A Kan Tallafin Mai – Minista

Kwamitin Wucin Gadi na Majalissar Wakilai Domin Bincikar Tallafin Mai na Tsakanin shekarar 2013 zuwa 2022, a jiya Alhamis ya titsiye Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed kan biyan kudin tallafin mai da gwamnatin tarayya ke yi.

Ministar ta bayyana cewa, gwamnati na kashe naira 283 na tallafi a kan kowacce lita ɗaya, abun da yake zama naira biliyan 18.397 a jimlace kowacce rana.

Zainab Ahmed ta kara da cewa, a hasashen man da za a dinga sha a duk a rana a shekarar 2023, matsakaici shine lita miliyan 64.96.

Ta kuma ce, idan akai la’akari da tazarar da ke tsakanin farashin mai kafin a sanya tallafi na naira 448.20k a kan kowacce lita da kuma farashin naira 165 da gwamnati ke siyar da man za a gane cewa gwamnatin zata biya tallafi na naira 283.2k a kan kowacce lita a shekarar.

Wannan na nuni da cewa, a kullum gwamnati zata na biyan naira biliyan 18.397 na tallafin, abun da a shekara ɗaya zai kai naira tiriliyan 6.71.

Ministar ta kara da cewa, wancan hali da akai hasashen za a shiga a shekarar 2023, shine halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Comments
Loading...