For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Apps 173 Na Bayar Da Bashi

Hukumar Kula Da Gasasseniya Da Kare Hakkin Mai Saye ta Gwamnatin Tarayya, FCCPC, ta amince da manhajojin yanar gizo na bayar da bashi a Najeriya har guda 173.

Cikin guda 173 da aka amincewa, 119 sun samu cikakkiyar amincewa, yayinda 54 suka sami amincewa da wucin gadi.

Bayan da manhajoji masu bayar da bashi suka fara cin zarafin ‘yan Najeriya, FCCPC ta fara aikin yin rijista ga manhajojin domin kare ‘yan Najeriya daga musgunawar wadannan manhajoji.

Wadansu daga cikin manhajojin bayar da bashin da suka samu sahhalewar hukumar sun hada da Branch International Financial Services Limited, Fairmoney Micro Finance Bank, Pivo Technology Limited, Renmoney Microfinance Bank Limited, Carbon Microfinance Bank Limited, Creditwave Finance Limited da sauransu.

Daga yanzu dai, dukkan wata manhajar bayar da bashin da ba ta samu sahhalewar FCCPC ba, Google zai cire ta daga Play Store ta yanda ba za a kara samun damar sauke ta ba.

Da ma, a watan November da ya gabata, Google Play ya sanar da sabunta Tsarin Samar da Manhajoji a Kan sa, wanda a ciki ya bukaci dukkan manhajoji masu bayar da bashi a Nigeria, India, Indonesia, Philippines da Kenya da dole su bi ka’idojin da aka shinfida.

Comments
Loading...