For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Hutun Bikin Babbar Sallah Na Kwanaki 2

Domin aiwatar da bukukuwan Babbar Sallar bana, Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin 11 da Talata 12 ga watan Yuli, 2022 a matsayin ranakun hutu.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar, Dr. Shuaibu Belgore ya fitar.

Aregbesola wanda ya taya dukkanin Musulmi da sauran ƴan Najeriya na gida da na waje murnar zagayowar bikin sallar, ya kuma kira ga al’umma da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in nemawa ƙasa zaman lafiya da ci gaba.

“Ina kira ga Musulmai da su yi koyi da halayen nuna soyayya, zaman lafiya, mutunci, sadaukarwa kamar yanda Manzon Allah SallalLahu Alaihi wa Sallam ya nunar, sannan su yi amfani da lokacin wajen yi wa ƙasa addu’ar fatan samun zaman lafiya, haɗinkai, ci gaba da kuma samun daidaiton al’amura duba da matsalolin da muke fama da su a halin yanzu.

Comments
Loading...