Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a 21 da Litinin 24 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin ranakun hutun Karamar Sallah a Najeriya.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hutun a madadin Gwamnatin Tarayyar, kamar yanda jawabin Babban Sakataren Ma’aikat’r Harkokin Cikin Gida, Dr. Shuaibu Belgore ya saki a yau Laraba.
A jawabin, Ministan ya taya al’umar Musulmi murnar kawo karshen watan Ramadana cikin nasara.
Aregbesola ya kuma yi kira ga Musulmi da su yi koyi da halayen tausayi, soyayya, juriya, zaman lafiya, kankan da kai, sadaukarwa da kuma kyautata mu’amala kamar yanda Manzon Allah SallalLahu Alaihi wa Sallam ya koyar.
Aregbesola ya bayar da tabbacin cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana shirya tsaf domin tabbatar da mika mulki ga sabuwar gwamnati bayan kammala zabubbuka.
Ya kuma tabbatar da kokarin gwamnati na samar da tsaro ga rayuka da dokiyoyin ‘yan Najeriya da baki ‘yan kasashen waje.
Aregbesola ya kuma yiwa Musulmi murnar zagayowar bikin Karamar Sallah tare da addu’ar samun zaman lafiya da albarka daga wajen Allah Mai Girma.