For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Hutun Kirsimeti Da Na Sabuwar Shekara

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar Litinin 26 da Talata 27 ga watan Disamba, 2022 a matsayin ranakun hutun bukukuwan Kirsimeti na bana.

Haka kuma, ranar Litinin, 2 ga watan Janairu na 2023, ita ma an bayyana ta a matsayin ranar hutun bukukuwan sabuwar shekara.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayar da sanarwar a jiya, a wata takarda da Babban Sakataren Ma’ikatarsa, Dr. Shuaib Belgore ya sanyawa hannu.

Aregbesola ya yi kira ga Kiristocin Najeriya da su yi anfani da lokacin bukukuwan wajen yin addu’o’in samun waraka daga matsalolin tsaron da ke addabar kasar nan.

Comments
Loading...