Gwamnatin Tarayya ta dakatar da sanannen shirin nan na tattaunawa, Idon Mikiya na gidan radiyon Vision FM.
Rahotanni sun ce, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ne saboda kalubalantar gwamnatin Najeriya da shirin yake yi.
Hukumar Gudanarwa ta Vision Media Services yau a Abuja ta karbi takarda da Ma’aikatar Yada Labarai da take sanar da ita cewa, shirin nan na tattaunawa mai suna Idon Mikiya ya dakata.
Hukumar, kamar yanda ta tabbatarwa NIGERIAN TRACKER ta bakin daya daga manajojinta, Shuaibu Mungadi, an bayyana cewa, Vision Media Services ta kuma karbi wani umarnin daga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya da ta dakatar da cigaba da gabatar da shirin na Idon Mikiya.
Shirin Idon Mikiya dai shiri ne da manyan ‘yan jaridu kuma mamallaka gidan radiyon Vision FM ke gabatarwa a Abuja, wadanda suka hada da Umar Faruk Musa, Shuaibu Mungadi da Abubakar kabiru Matazu.
Ana sanya shirin a ranakun Latinin, Talata da Alhamis a tashoshin Vision Media Services guda 7 da ke fadin Najeriya.
Batutuwan da aka fi tattaunawa a shirin sun shafi tsarin gudanar da gwamnati, kashe kudade a gwamnati wanda ya hada da bibiyar kasafin kudi da kuma matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan.
(NIGERIAN TRACKER)