For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ta Kirkiro Sabuwar Ma’aikata, Ta Nada Shugaba

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da kirkirar sabuwar ma’aikatar gwamnati mai suna Nigeria Data Protection Bureau, NDPB.

Kirkirar ma’aikatar ta samo asali ne daga bukatar yin hakan da Ministan Ma’aikatar Sadarwa, Dr. Isah Ali Pantami ya yi.

A jawabin da mai taimakawa Pantami kan kafafen yada labarai, Uwa Suleiman, ta raba kuma TASKAR YANCI ta samu, an kirkiri ma’aikatar NDPB ne dai-dai da tsarin cigaban duniya kuma za ta temaka wajen kare sirrikan kasa da sauran abubuwa.

Sanarwar ta kara da cewa, nasarar gudanar da tsarin cigaban tattalin arziki ta hanyar yanar gizo ya jawo karuwar bukatar amfani da kundayen ajjiye bayanai da kuma karuwarsu a kasar.

“Wannan ya kara girman muhimmancin samuwar ma’aikatar da za ta mayar da hankali kan kare bayanai da kuma sirrika”.

“Haka kuma, samar da dokar Nigeria Data Protection Regulation, NDPR, a watan Janairun 2019, a matsayin doka cikin dokokin kula da ma’aikatar National Information Technology Development Agency (NITDA) Act 2007, ta kara yawan fahimtar cewa akwai bukatar kariya ga bayanai da kuma sirrika.”

Shugaba Buhari ya kuma amince da wanda Dr. Isah Ali Pantami ya gabatar masa a matsayin shugaban ma’aikatar na kasa mai suna Dr. Vincent Olatunji.

Olatunji dan asalin jihar Ekiti ne kuma a lokacin da aka amince da nadinsa, yana matsayin Daraktan Sashin Kula da Gudanar da Gwamnati ta yanar gizo a hukumar NITDA.

Comments
Loading...