For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ta Nada Shugabannin Sabbin Jami’o’i 4 Da Ta Samar

Duba da ka’idoji, Gwamnatin Tarayya ta sanar da nadin jagorori (principal officers) na sabbin jami’o’i 4 ta samar a kasar.

Ma’aikatar Ilimi ta kasa ce ta sanar da nadin a wata sanarwa da ta gabatar ga manema labarai yau a Abuja ta hannun Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar, Mr Ben Goong.

Sanarwar ta ce, a Federal University of Technology, Babura da ke Jihar Jigawa an nada Farfesa Sabo Ibrahim a matsayin Shugaban Jami’ar, yayin da Fatima Mohammed ta zama Rijistara, sai kuma Ibrahim Alhassan ya zama Bursar da kuma Abashe Atiku a matsayin Librarian.

A Federal University of Technology, Ikot Abasi, da ke jihar Akwa Ibom kuma an nada Farfesa Leo Daniel a matsayin Shugaban Jami’ar, sai kuma Offiongita Nkang a matsayin Rijistara, an kuma nada Mbobo Frasmus Mbobo a matsayin Bursar da kuma Farfesa Philip Akor a matsayin Librarian.

A Federal University of Health Sciences, Azare da ke jihar Bauchi kuma, an nada Farfesa Bala Audu a matsayin Shugaban Jami’ar, sai kuma Ali Adamu a matsayin Rijistara da kuma Mohammed Lawan a matsayin Bursar sai Dr Bappah Magaji a matsayin Librarian.

Sanarwar ta kara da cewa, a Federal University of Health Sciences, lla Orangun, da ke jihar Osun kuwa, an nada Farfesa Akeem Lasisi a matsayin Shugaban Jami’ar, sai kuma Kassim Babamale a matsayin Rijistara da kuma Adelani Oyewale a matsayin Bursar sai kuma Bukky Asubiojo a matsayin Librarian.

Sanarwar ta kuma baiyana cewa, an yi nadin ne domin a gaggauta fara gudanar da jami’o’in.

A shekarar 2021 ne dai, Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya ya rawaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta kirkiro da sabbin jami’o’i guda hudu domin magance matsalar karancin ilimin kimiyyya da fasaha, ilimin likitanci da kuma ilimin sanin sinadaran kara lafiya.

(NAN)

Comments
Loading...