Gwamnatin Tarayya ta sanar da rage lokacin aiki ga ma’aikatanta a faɗin Najeriya saboda su samu damar goyawa Ƙungiyar Wasan Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, Super Eagles.
Gwamnatin ta rage lokacin aikin ne na yau Talata 29 ga watan Maris, 2022, inda maaikata zasu tashi aiki da misalin ƙarfe 1:00 na rana saɓanin ƙarfe 4:00 na yamma da aka saba a koyaushe.
Ƙungiyar Super Eagles dai zata buga wasan neman shiga gasar cin kofin duniya ne da Ƙungiyar Black Stars ta ƙasar Ghana a yau ɗin.
Za a buga wasan ne a filin wasa na Moshood Abiola Stadium da ke Abuja da misalin ƙarfe 6:00 na yammaci a Najeriya.
Shugabar ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dr. Ngozi Nwudiwe ce ta sanyawa sanarawar hannu, ta kuma yi kira ga manyan sakatarorin gwamnati da su yaɗa wannan sanarwa.
