Gwamnatin Tarayya ta saki wadanda ake zargin ‘yan haramtacciyar kungiyar Masu Neman Kafa Kasar Biafra, IPOB ne, wadanda Sojojin Najeriya suka kama a ranar 27 ga Fabarairu na 2020 a kauyen Kogin Imo da ke Jihar Abia.
Wadanda ake zargin, Sunday Nwafor dan shekara 59; Uzonwanne Ejiofor, dan shekara 48; da kuma Wilfred Dike dan shekara 36, an kullesu ne a 14 Brigade Nigerian Army da ke Ohafia a Jihar Abia tsawon shekara biyu.
Haka kuma, Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International reshen Najeriya ta yi maraba da hukuncin sakin mutane ukun.
A wata sanarwa da ta saki a jiya Laraba, Amnesty International ta yi kira ga gwamnati da ta samar da bayanai kan yanayin da sauran mutanen da suka bace da kuma wadanda suke tsare a wajen jami’an tsaro.