For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Kashe Wa Ɓangaren Ilimi Kaso 25% Na Kasafin Kuɗi

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewar, Gwamnatin Tarayya ta shirya kashewa ɓangaren ilimi kaso 25 cikin ɗari na kasafin kuɗin kowacce shekara matuƙar akwai tsare-tsaren da su tabbatar da buƙatar kuɗaɗen.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya bayyana a Abuja a lokacin ƙaddamar shiri kan bunƙasa ilimi da matasan yankin Arewa maso Yamma wanda zai laƙume kuɗi yuro miliyan 40.

Ya ce, duk wani yunƙuri da za ai na durƙusar da ilimi da rashin nuna kulawa ga matasa zai jawo wa Najeriya matuƙar matsala a ɓangaren walwala da kuma tsaro.

Farfesa Mamman ya kuma buƙaci gwamnoni da su bayar da fifiko wajen bunƙasa ilimi da rayuwar matasa, inda ya ce, tsarin inganta ilimi da za fitar a ƴan kwanaki masu zuwa ya zo daidai da tsarin da Tarayyar Turai ta kawo.

Comments
Loading...