For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 13.8 Domin Biyan Fanshon Tsoffin Shugabanin Kasa Da Sauransu A 2023

Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta ware kudi Naira Biliyan 13,805,814,220 a kudirin kasafin kudin shekarar 2023 domin biyan fansho ga tsoffin shugabanin kasa, tsoffin mataimaka shugaban kasa, tsoffin shugabannin mulkin soja, tsoffin shugabannin ma’aikata, tsoffin manyan sakatarori da kuma sauran tsoffin shugabannin ma’aikatu.

Cikin wadanda zasu mori wadannan kudade akwai tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, da kuma tsoffin mataimaka Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Namadi Sambo.

A bangaren tsoffin shugabannin mulkin soja akwai Janar Yakubu Gowon, Janar Ibrahim Babangida, Janar Abdussalami Abubakar da Shugaban Ma’aikata, Commodore Ebitu Ukiwe, dukkaninsu masu ritaya.

Kudirin kasafin kudin ya nuna cewa, an ware Naira Biliyan 2.3 a matsayin fanshon shekara daya na tsoffin shugabannin su 8.

Kudirin kasafin kudin kuma ya yi nuni da cewa, an ware Naira Biliyan 10.5 a matsayin kudin fanshon tsoffin shugabannin ma’aikata da manyan sakatarori, yayin da kuma aka ware Naira Biliyan 1 a matsayin kudin sallamar shugabannin ma’aikatun gwamnati.

Comments
Loading...