Gwamnatin Tarayya na shirin buɗe boda tare janye harajin shigo da wasu muhimman kayan abinci ta iyakokin ƙasa da kuma na ruwa.
TASKAR YANCI ta tattaro cewar, wannan hukunci ya fito ne saboda buƙatar da ake da ita na samun sauƙin farashin kayayyakin abinci waɗanda suka yi tashin gwauron zabi, suka sanya rayuwar ƴan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Haka kuma, Ƙungiyar Ƴankasuwa, Masu Masana’antu, Masu Haƙar Ma’adanai da Manoma ta NACCIMA haɗi da Cibiyar Bunƙasa Kamfanoni Masu Zaman Kansu ta CPPE, a wani martani da suka fitar, sun yabawa gwamnati bisa wannan yunƙuri, inda suka ce hakan zai zama mai tasiri kan hauhawar farashi.
Wata majiya ta bayyana cewar, kayayyakin abinci da lamarin zai shafa waɗanda suka haɗa da shinkafa da wake, zasu kwashe kwanaki 150 ana shigo da su ba tare da haraji ba.
Majiyar ta ƙara da cewa, gwamnati ta gano gaskiyar cewa, farashin kayan abinci, a watannin da suka gabata, sun yi matauƙar ƙaruwa, lamarin da ya jefa rayuwar al’ummar Najeriya cikin matuƙar ƙunci.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, NBS, ta bayyana hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya da alƙaluman da ke nuni da tashi har zuwa kaso 40.66 cikin 100.