For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnoni, Atiku, Kwankwaso Da Sauransu, Sun Jinjinawa Tinubu

Sanannun ƴan Najeriya da suka haɗa da ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar sun taya Asiwaju Bola Tinubu murnar samun tikitin yi wa jam’iyyar APC takara.

Haka kuma, gungun mutane kamar Zauren Jam’iyyun Najeriya (Conference of Nigeria Political Parties, CNPP) da kuma Haɗakar Shugabannin Matasa na Kudu maso Gabas (Coalition of Southeast Youth Leaders) sun yi maraba da nasarar Tinubu, inda suka ce, ba su tattamar cewa, zai gyara Najeriya idan har aka zaɓe shi Shugaban Ƙasa.

Sauran manyan mutanen da suka taya Tinubu murnar sun haɗa da; ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin tutar jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso; Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan; Kakakin Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila; Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu; Gwamnan Jihar Osun, Adegboyega Oyetola; Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi; Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun; Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje; Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq; da kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa.

A cikin masu taya murnar akwai, tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Gbenga Daniel; Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Ovie Omo-Agege; Mataimakin Kakakin Majalissar Wakilai, Ahmad Wase; Shugaban Majalissar Dokoki ta Jihar Lagos, Mudashiru Obasa; Sanata Andy Uba; Ƙaramin Ministan Aiyuka, Festus Keyamo (SAN) da kuma Florence, matar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

Sun bayyana cewa nasarar Tinubu ta samo asali ne daga ƙwazonsa da jajircewarsa da kuma iya siyasa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana zaɓen fitar da gwani na APC a matsayin “zazzafan faɗa”.

Comments
Loading...