For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnoni Da Kungiyar Kwadago Na Da Tantama Kan Man Da Ake Sha A Najeriya

Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya, NGF da Kungiyar Kwadago, NLC a ranar Laraba sun kalubalanci Kamfanin Dillancin Mai na Najeriya, NNPC kan abun da suka kira da nuna halin ko in kula ga al’amuran tallafin mai.

NGF da NLC, kamar yanda Shugaban Al’amuran Yada Labarai na NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fada a matsayin wani daga cikin matsayar da aka samu a zaman tattaunawa a Abuja. Ya ce suna zargin adadin man da ake sha wanda NNPC ta fada.

Kamar yanda shugabannin kungiyar kwadago da gwamnoni suka kalubalanci NNPC, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, kamfanin na NNPC ya kabatar da kasafin kashe kudi naira tiriliyan 3 wajen biyan tallafi a shekarar 2022.

Haka kuma a dai ranar Larabar, Majalissar Wakilai ta ce, za ta binciki alkaluman da ke nuni da yawan man fetur din da ake sha a Najeriya da kuma yanayin matatun man kasar guda hudu.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Gwamnatin Tarayya ta dage yunkurinta na janye tallafin mai a watan Yuni. Haka kuma ta dage fara amfani da Dokar Kamfanin Man Fetur har sai bayan watanni 18.

KU KARANTA: Kungiyar Kwadago Ta Janye Zanga-Zangar Da Ta Shirya Gudanarwa

Da suke duba abubuwan da ke faruwa a bangaren mai, kungiyar gwamnoni da shugabannin kwadago sun amince cewa gaskiyar abin da ke cikin maganar cire tallafin mai wata aba ce da kumbiya-kumbiya ta dabaibaye.

Sun zargi NNPC da kasancewa kan gaba wajen nuna halin ko in kula kan abubuwan da ke faruwa a al’amarin.

Barkindo, a jawabin sa ya bayyana cewa, Shugaban Kungiyar Gwamnoni, Kayode Fayemi, ya tabbatar da cewa tattalin arzikin kasa yana cikin halin-ha’ula’i saboda haka, ya zama dole kungiyoyin biyu su binciki kididdigar NNPC da nutsuwa.

“Fayemi ya fadawa shugabannin kungiyar kwadago cewa, cire tallafi wani abu ne da ake cigaba da tattaunawa ba wai kawai iya cikin kungiyar gwamnoni ba, har ma ga dukkannin ‘yan kasa.

“Akwai tambayoyi da dama da suka shafi gaskiyar da ke tattare da cire tallafin mai a kasa, kuma ku lura, NGF da NLC za su iya yin aiki tare wajen gabatar da mafutar da za ta warkar da matsalolin tattalin arziki tare da samar da walwala ga ‘yan Najeriya.”

(PUNCH)

Comments
Loading...