Gwamnonin APC na yankin Arewa sun ƙara jaddada matsayarsu ta jam’iyyar APC ta miƙa takarar Shugaban Ƙasa zuwa yankin Kudu jam’iyyar.
Gwamnonin sun baiyana hakan ne bayan ganawarsu da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a yau Litinin.
Matsayar gwamnonin dai ta saɓa da matsayar da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu ya sanar na cewa jam’iyyar APC ta amince da Sanata Ahmad Lawan a matsayin ɗan takara na maslaha.
Abdullahi Adamu dai, a yau Litinin, a lokacin zama da sauran shugabannin jam’iyyar na ƙasa, ya sanar da sunan Sanata Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar da aka amince da shi a matsayin maslaha.
Wannan matsaya ta Abdullahi Adamu dai, ta saɓawa abin da gwamnoni 11 na jam’iyyar daga yankin Arewa suka zartar, inda suka buƙaci APC da ta miƙa takarar Shugaban Ƙasa zuwa yankin Kudu.
Gwamnonin na APC daga Arewa dai, sun gana Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a yau Litinin da rana, inda suka jaddada masa cewa su dai zasu goyi bayan ɗan takara ne kaɗai daga yankin Kudu.
Gwamnonin da suka halarci zaman da Shugaba Buhari sun haɗa da: Abubakar Bagudu na Jihar Kebbi, Simon Lalong na Jihar Plateau, Abubakar Badaru na Jihar Jigawa, Aminu Masari na Jihar Katsina, Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, Bello Matawalle na Jihar Zamfara, Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, Abubakar Bello na Jihar Niger, Yahaya Inuwa na Jihar Gombe, Babagana Zulum na Jihar Borno, Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, da Mai Mala Buni na Jihar Yobe State.
Gwamnan Jihar Plateau, wanda shine Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, Simon Lalong, ya yi magana a madadin sauran gwamnonin, inda ya ce, gwamnonin na Arewa sun tabbatar da matsayarsu ta ɗan takara ya fito daga Kudu.
Ya ce, gwamnonin sun sanar da Shugaban Ƙasa dalilansu na goyon bayan ɗan takarar da zai fito daga yankin Kudu domin yi wa jam’iyyarsu takara a shekarar 2023.
Shima Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce, matsayar ta gwamnonin Arewa na APC ita ce ƙarshe, cewa iya ɗan takarar da ya fito daga yankin Kudu zasu goyawa baya.
El-Rufa’i ya ce, ra’ayin Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello na ƙin zuwa zaman, da ƙin shigarsa cikin amincewar sauran gwamnonin, ba zai canza matsayarsu ba, inda ya ƙara da cewa, shi ɗaya ne tilo cikin gwamnoni 14 da ke goyon bayan kai takara yankin Kudu.