Gwamnonin jamíyyar APC sun mika sunayen masu neman takarar Shugaban Kasa guda 5 cikin 23 domin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zabi daya daga ciki a matsayin dan takara na maslaha.
Wata majiya mai karfi ta sanar da jaridar DAILY TRUST cewa, gwamnonin sun mika sunayen ne a sanyi safiyar yau Talata.
Sunayen da aka mika kamar yanda majiyar ta sanar sun hada da, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, tsohon Gwamnan Jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da kuma Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi.
Gwamnonin bayan ganawa da Shugaba Buharin sun ce, zasu koma fadar Shugaban Kasar bayan sun gana da Kwamitin Shugabancin Jam’iyyar na Kasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Jerin sunayen ya nuna cewa, gwamnonin sun zabo mutane dai-dai ne daga yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu da kuma mutane 3 daga yankin Kudu maso Yamma gwargwadon bukatarsu ta mika takara zuwa yankin Kudu.
A jiya ne dai, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da sunan Shugaban Majalissar Dattawa Ahmad Lawan a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar, abin da ya saba da fatan gwamnonin.