Gwamnan Jihar Nassarawa, Abdullahi Sule ya ce, gwamnonin jam’iyyar APC sun magance saɓanin da ke tsakaninsu gabanin taron zaɓen shugabannin da za a gudanar ranar 26 ga watan Maris ɗin nan.
Gwamna Abdullahi Sule, wanda shine Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Babban Taron Zaɓen Shugabannin APC da za a gudanar ranar 26 ga watan Maris, ya baiyana hakan ne a wata sanarwa da Alhaji Garba Shehu, wanda shine Sakataren Kwamitin ya sanyawa hannu a ranar Litinin a Abuja.
Gwamna Abdullahi Sule ya yi wannan magana ne a lokacin ƙaddamar da kwamitin yaɗa labaran da kuma ƙananan kwamitocin da ke ƙarƙashinsa a Abuja.
“Shugabancin Jam’iyya ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni da sauran mambobin Kwamitin Riƙo, na yin duk mai yiwuwa wajen damawa da kowa.
“Na yi imanin cewa, ita ce hanya ɗaya tilo ta samun nasarar gudanar da zaɓen jam’iyya na ƙasa da samun nasara a zaɓuɓɓuka. Mun yarda da haɗin kai cikin mabanbanta ra’ayi, kuma wannan shine sirrin taron zaɓenmu,” in ji shi.
Kusan masu zaɓe 4,000 daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja ake sa ran zasu zaɓi sabbin shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa.