For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnonin Arewa 10 Na APC Da Suka Ce Jam’iyyar Ta Bayar Da Takarar Shugaban Ƙasa A Kudu

Gwamnonin Arewa guda 10 ne suka amince da cewa, jam’iyyar APC mai mulki ta miƙa takarar Shugaban Ƙasa ga yankin Kudancin Najeriya, sannan suka bukaci duk masu neman takara daga Arewa su janye.

Gwamnonin sun ɗau wannan matakin ne a wani zama da suka yi jiya Asabar da daddare a Abuja.

Gwamnonin da suka sanyawa takardar sanar da matsayar tasu hannun sune: Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari; Gwamnan Jihar Niger, Abubakar Sani Bello; Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Umara Zulum; Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Yahaya; da Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle.

Sauran gwamonin sune: Gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong; Gwamnan Jihar Kano, Dr. Umar Ganduje; Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; da kuma tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko.

Sanarwar bayan zaman yanke hukuncin ta ce, “Gwamnonin APC da manyan ƴan siyasa daga Arewacin Najeriya, a yau sun haɗu domin su duba yanayin siyasa tare da ƙara baiwa jam’iyyarmu goyon baya wajen samar da ingantaccen shugabanci duk da irin wannan hali na ƙalubale da ƙasa ke ciki.

“A lokacin tattaunawarmu, mun yi maraba da gaiyatar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki, kan cewa su bayar da gudunmawarsu wajen samar da ƙwaƙƙwaran ɗan takarar Shugaban Ƙasa ga jam’iyyar APC.

“Bayan duba na tsanaki, muna fatan sanar da ƙaƙƙarfar matsayarmu cewa, bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗebe shekaru takwas a ofis, ɗan takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023 ya zama ɗaya daga cikin ƴan jam’iyyarmu da ke jihohin yankin Kudancin Najeriya.

Comments
Loading...