Kungiyar Gwamnonin Arewa za su yi wani taron gaggawa a yau Litinin don tattauna batutuwan da suka shafi Harajin VAT.
Jaridar PUNCH ta gano cewa taron da aka shirya, wanda gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai zai zama mai saukar baki, shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, shine zai jagoranci zaman.
Ko’odinetan sakatariyar kungiyar gwamnonin Arewa kuma sakataren gwamnatin jihar Filato, Farfesa Danladi Atu, ya tabbatar yin da taron da aka shirya a wata hira da jaridar PUNCH a Jos ranar Lahadi.
Atu ya fadi haka ne yayin da wasu manyan lauyoyi suka kai karar Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, kan kalamansa na baya-bayan nan cewa babu wata jiha da ke da ikon yin da’awar karbar harajin VAT a kasar.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Fatakwal ta yanke hukunci a watan da ya gabata cewa jihar Ribas na da ikon karbar Harajin VAT a cikin hurumin ta.
Amma Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Tarayya ta nufi kotun daukaka kara don kalubalantar hukuncin.
A kotun daukaka karar, jihar Legas ta shigar da bukatar cewa ya kamata a hada ta da jihar Ribas a matsayin wanda ake tuhuma a karar da FIRS ta shigar.
Kotun daukaka kara ta umarci wadanda ke cikin karar su ci gaba da kasancewa a yanayin da ake har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin daukaka kara.
Malami, a cikin wata hira da gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, ya ce tsarin karbar harajin VAT a cikin kasar yana cikin kebantattun jerin dokokin da suka shafi gwamnatin tarayya, ya kara da cewa Majalisar kasa ce kadai ke da ikon yin doka a kan VAT.
Ya ce, “Kamar yadda kuka sani, batun harajin VAT batu ne a cikin kebabbun jerin dokoki. Kuma abin da ake nufi da kasancewa cikin jerin abubuwan da aka ware na majalisar dokoki shine Majalisar Tarayya ce kawai za ta iya yin doka a kanta. Tambayar da watakila za ku so ku yi ita ce ko akwai wata doka ta kasa da ta ba wa jiha ikon karbar Harajin VAT? Kuma amsata ita ce ‘a’a’ babu.”