For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnonin PDP na kudancin Najeriya sun sauya matsayi kan G5

Gwamnonin Jam’iyyar PDP da suka fito daga yankin Kudu maso kudu a Najeriya, sun yanke hukuncin ganawa da kungiyar gwamnoni 5 ta G5 da ke karkashin Nyesom Wike da suka bijire wa matsayin jam’iyyar bayan zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasar da Atiku Abubakar ya samu nasara.

Bayan wata ganawar da suka yi a Jihar Bayelsa, Gwamnonin sun ce zasu gana da kungiyar ta G5 wadda ta dade tana tauna tsakuwa dangane da zaben da kuma bukatar ganin shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya sauka daga kujerarsa saboda kai kujerar takaran shugaban kasa arewa.

Kungiyar ta G5 wadda ta kunshi Gwamna Wike na Rivers da Samuel Ortom na Benue da Ifeanyi Ugwanyi daga Enugu da Okezie Ikpeazu daga Abia da kuma Seyi Makinde daga Oyo sun kekashe kasa cewar dole sai jam’iyyar ta biya musu bukatunsu kafin yiwa Atiku yakin neman zabe mai zuwa.

Bayan kwashe watanni 6 ana taku saka da kuma musayar kalamai tsakanin kungiyar ta G5 da bangaren Jam’iyyar, Gwamnonin na yankin kudu maso kudu sun ce zasu shiga tsakani domin dinke barakar da aka samu, lura da cewar lokacin zabe na dada karatowa.

Gwamnan Bayelsa da ya karbi bakuncin taron ya jaddada goyan bayansu ga takarar Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa wanda shima ya samu halartar taron.

RFI Hausa

Comments
Loading...